Dariye Ya Ƙaryata Batun Tsayawar Sa Takara, Bayan Fitowa Daga Gidan Yari

Gwamnan Filato Simon Lalong ya jagoranci wata babbar tawaga daga jihar domin ziyarar tsohon gwamnan jihar Joshua Chibi Dariye da tsohon gwamnan Taraba Rabaran Jolly Nyame bayan an sako su daga gidan yari.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta rawaito cewa ziyarar ta biyo bayan afuwar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya yi musu.

Lalong tare da matarsa, Regina, ‘yan majalisar dokoki ta kasa da kuma ‘yan majalisar zartarwa ta jihar sun fara ziyartar gidan Cif Dariye ne domin godiya ga Allah da samun yancin shaƙar iska.

Ya shaida wa Dariye cewa yayin da al’ummar jihar suka samu labarin sakinsa sun cika da farin ciki domin tun lokacin da suka shiga gidan yarin suke yi masa addu’ar samun sauki.

Gwamnan yayin da ya ke yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yafewa Dariye, ya ce wannan lokaci ne da Cif Dariye ya kamata ya yi tunani tare da gafartawa mutanen da ka iya bata masa rai kamar yadda ya saba yi a lokutan kalubalen da ya fuskanta a baya.

Da yake mayar da martani, Dariye ya ce yana matukar godiya ga Allah da ya sa aka sake shi tare da yin amfani da mutane irin su Gwamna Lalong da Shugaba Buhari wajen ganin an sake shi.

Dariye ya kuma karyata rade-radin da ake yadawa na cewa ya fito takarar Sanata yana mai bayyana hakan a matsayin labari mara tushe kuma ba gaskiya ba ne domin bai sayi fom ba ko kuma ya yi wani abu a kan haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Share via
Copy link
Powered by Social Snap