NNPC Ta Ƙaddamar Da Wata Manhajar Da Za Ta Sa Ido Kan Ɓarayin Mai

NNPC Ta Ƙaddamar Da Wata Manhajar Da Za Ta Sa Ido Kan Ɓarayin Mai

Kamfanin mai na kasa NNPC ya kaddamar da manhajar da zata dinga sa ido kan masu satar danyan mai a ranar juma’a.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaito cewa an kaddamar da manhajar ne a Abuja, ya yin da kamfanin ya ke sabon ta yarjejeniyar PSCs tsakanin kamfanin na NNPC da abokan kasuwan cin sa.

Domin bada bayani za’a iya shiga shafin yanar gizo ta ‘stopcrudetheft.com ko kuma amfani da manhajar ta wayar hannu.

Ya yin jawabin sa a gurin kaddamar war, shugaban kamfanin NNPC na kasa Malam Mele Kyari, ya ce magance matsalar satar danyan mai abu ne da yake da wahalar gaske, dole ne a hada hannu da mutanan gari da kuma sauran jami’an tsaro domin magance matsalar.

“Har yanzu masu star danyan mai da guraren da ake ta ce mai ba tare da izinin gwamnati ba sunan suna cigaba da cin karansu ba babbaka.”

“Ba jimawa sai da sojojin ruwa na kasa suka kama masu satar man da kuma ma masu guraren tace man na haram tatciyar hanya, na yabawa sojojin ruwan sosai bisa wannan babban aiki da suka yi.” Injishi.

Ya kara da cewa kamfanonin tace mai na kasashen waje, da ake kai man da aka Sata a Najeriya, yazama dole su tabbata suna siyan mai daga hannun gwamnati, idon ba haka suma zamu dinga hadawa da su wajan hukunta barayin.

Ya kara da cewa an samar da manhajar ne domin mutane da kuma sauran hukumomin gwamnati su dinga bada bayanai kan masu satar mai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Share via
Copy link
Powered by Social Snap