Manyan Ƙasashe Huɗu Sun Sanar Da Yiwuwar Kai Mummunan Hari A Abuja

Manyan Ƙasashe Huɗu Sun Sanar Da Yiwuwar Kai Mummunan Hari A Abuja

 

Gwamnatocin kasashen Jamus da Bulgeriya da Ireland da kuma Denmark sun gargadi ‘yan kasarsu kan tafiye-tafiye marasa mahimmanci zuwa Abuja, babban birnin tarayyar kasar nan saboda karuwar hare-haren ta’addanci.

Shawarwarin tafiye-tafiyen ya zo ne kwanaki kadan bayan Amurka, Birtaniya, Australia da Kanada sun yi gargadin yiwuwar kai harin ta’addanci a Abuja.

Tuni dai gwamnatin tarayya ta bakin Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ta yi watsi da shawarwarin inda ya ce ita ma Amurka ba ta da zaman lafiya.

Da aka tuntube shi a ranar Alhamis don jin ta bakinsa kan matakin da Bulgaria, Jamus, Ireland da Denmark suka dauka, Lai Mohammed ya roki Daily Trust da ta aiko masa da “Hanyoyin labarun Denmark, Jamus, Bulgariya da Ireland domin na daidata martanina.”

Daily trust ta ruwaito cewa, ofisoshin jakadanci sun jera wuraren da suka hada da makarantu, gine-ginen gwamnati, otal-otal, kasuwanni, manyan kantuna, mashaya, wuraren wasannin motsa jiki, tashoshin sufuri, wuraren tabbatar da doka, gidajen abinci, wuraren ibada da kuma kungiyoyin kasa da kasa.

Daga ingantattun majiyoyin diflomasiyya cewa wasu kasashe sun yi daidai da matsayin Amurka bayan wasu tarurrukan musayar bayanan sirri da “tabbatar da ba za ta iya tantancewa ba na hadarin da ke tafe.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram