Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP, Alkali Baba Usman, ya gargadi kasashen ketare kan gargadin yuwuwar kai hare-haren ta’addanci a Najeriya.
IGP ya yi wannan magana ne a ranar Asabar yayin da yake kaddamar da ofishin ‘yan sanda a Ibusa, dake karamar hukumar Oshimili ta Arewa a jihar Delta.
Usman ya ce ya kamata kasashen ketare su daina sanar da jama’a game da yuwuwar kai hare-haren.
Shugaban ‘yan sandan ya kuma kara da cewa, sanarwar ta’addancin kwanan nan ya kamata a bai wa ‘yan sanda ne ita kai tsaye, ba jama’a ba.
Sai dai IGP din ya baiwa jama’a dake fadin kasar nan, tabbacin kare lafiya da dukiyoyin su.
Idan ba a manta ba, Gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun fitar da wata sanarwar da ke nuna yuwuwar kai wasu hare haren ta’addanci a babban birnin Tarayya Abuja.
A cikin shawarwarin da Kasashen suka bada, sun bukaci ‘yan kasashen su da su kaurace wa Abuja saboda hare-haren da ‘yan ta’adda suka shirya kai wa.