Najeriya na asarar akalla gangar danyen mai 700,000 saboda barayi a kullum.
Ƙaramin ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva ne ya bayyana hakan a Delta Asabar.
Ya bayyana hakan ne a wajen yaye daliban Cibiyar Koyar da tasarrufin Man Fetur (PTI) a shekarar 2002.
Ministan wanda ya samu wakilcin Ambasada Gabriel Aduda, babban sakatare a ma’aikatar albarkatun man fetur, ya ce gwamnatin tarayya na kokarin dakile wannan matsala.
Ya ce satar danyen man na ci gaba da illa ga bangaren musayar kudaden kasashen ketare a cikin kasar, wanda hakan ya taimaka wajen kara faduwar darajar Naira.
”Mummunan illar hakan shi ne raguwar samar da danyen mai da raguwar kudaden shiga na kasa,” inji shi.
Ya ce ma’aikatar man fetur za ta hada kai da majalisar dokokin kasar domin tabbatar da cewa an ba da cikakkiyar kulawa ga gyaran dokar kula da man.
Sylva ya ce cibiyar za ta iya samun ci gaba idan aka yi wa dokar kwaskwarima don baiwa cibiyar damar samun karin kudade.
Ya ce ma’aikatar ta bai wa PTI umarni a fannoni daban-daban na bincike kan amfani da kayan cikin gida wajen hako danyen mai, daina mu’amala da iskar gas da sayar da iskar gas da dai sauransu.