Gwamnatin Sokoto Za Ta Ƙarawa Malamai Albashi

Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya kaddamar da kwamitin da zai baiwa gwamnatin jihar shawara, kan irin albashin da ya kamata a biya shugabannin makarantun sakandare na gwamnati (Principals) a fa’din jihar Sokoto.

Kwamitin ta ƙunshi mutane irin su Alhaji Buhari Bello Kware, tsohon shugaban ma’aikata a matsayin shugaba sai mambobi da aka d’auko daga wurare da dama.

Aikin kwamitin ya hada da bada shawara akan wanne irin albashi ya kamata a biya su.

Kazalika, kwamitin zai bada shawara akan kudaden fansho da garatuti da alawus-alawus da kuma sauran hakkokin su.

Gwamna Tambuwal yace an kafa kwamitin na shugabannin sakandare kuma nan bada jimawa ba, za a samar da na makarantun firamare.

Ya kuma bada mako uku don su kammala aiki domin fara aiwatar da shawarwarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram