Jiragen Yaƙi Da Najeriya Ta Siyo Daga Turkiyya Sun Kusa Isowa

Jakadan Jamhuriyar Turkiyya a Najeriya Hidayet Bayraktar ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba jirage marasa matuka da jirage masu saukar ungulu daga Turkiyya za su iso Najeriya a wani mataki na karfafa tsarin tsaro a kasar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Bayraktar ya bayyana haka ne a yayin taron tunawa da ranar Jamhuriyar Turkiyya karo na 99 a Abuja.

Ya bayyana tallafin tsaro da Turkiyya ke baiwa Najeriya a matsayin wata nasara daga yarjejeniyar hadin gwiwa ta tsaro da kasashen biyu suka kulla a shekarar 2021.

Ya kara da cewa, Turkiyya na shirin baiwa Najeriya duk wani nau’i na tallafi a kokarinta na dakile barazanar tsaro ta hanyar amfani gogewarta da fasaharta ta fuskar tsaro.

Ya kuma kara da cewa, gwamnatin Turkiyya na kuma sa ran gwamnatin Najeriyar za ta yi abubuwanda suka dace kan kula da harkokin tsaro.

Dangane da alakar da ke tsakanin kasashen biyu, Bayraktar ya ce yana matukar alfahari da cewa, yarjejeniyar da aka kulla a shekarar 2021 da 2022 ya kasance wani babban ci gaba a dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Najeriya.

Kazalika ya kuma bayyana cewa, a halin da ake ciki na karuwar huldar kasuwanci, yana da yakinin cewa nan ba da dadewa ba Turkiyya za ta cimma burin da ta sa a gaba na zuba jarin dala biliyan 5 na hada-hadar kasuwanci tsakanin kasashen biyu da Najeriya.

Ana shi bangaren, Karamin ministan harkokin wajen Najeriya, Ambasada Zubairu Dada, ya ce Najeriya da Turkiyya sun habakar harkokin kasuwanci tun bayan ziyarar manyan jami’an kasashen biyu a shekarar 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram