Kada Ku Sake Ku Bar Mazajen Ku Su Zaɓi Wata Jam’iyya Ba APC Ba – Shugabar Matan APC

Mataimakiyar shugabar mata ta jam’iyyar APC, Zainab Ibrahim, ta yi kira ga mata da kada su bari mazajensu su zabi wata jam’iyya a zaben shekarar 2023 mai zuwa. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Ta yi wannan kiran ne a wajen kaddamar da ofishin yakin neman zaben kungiyar dake goyon bayan takarar Tinubu da Shattima na kasa baki daya wato HUM National Support Group for Tinubu/Shettima.

Taron dai ya gudana ne a Jiya Asabar a babban birnin tarayya Abuja.

Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Kashim Shettima ne ya jagoranci bude ofishin a hukumance.

Ta shawarci matan da su boye katin zaben mazajensu da kyau (PVCs) idan suka fahimci cewa, za su bata kuri’unsu ta hanyar zaben wata jam’iyyaar da ba jam’iyyar APC mai mulki ba.

“Wannan shine lokacin da ya kamata a hana PDP sakat, Ku tabbata (duk wanda mijinta bai shirya zaben APC ba) ta boye katin zaben shi na din din din.”

“Kar ki bari ya bata kuri’ar shi, Dole ne dukkan kuri’un majazajen mu su kasance na Jam’iyar APC ne” inji ta.

A nasa bangaren, mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa ta bangaren yankin Arewacin kasar nan, Sanata Abubakar Kyari ya yabawa kodinetan kungiyar, bisa kokarin da take yi na hada kan ‘yan Najeriya wajen marawa jam’iyyar baya da kuma zaben jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram