Masana Sun Yi Bincike, Sun Ce Za’a Samu Rigakafin Zazzabin Lassa Nan Da 2030

Masana Sun Ce Za’a Samu Rigakafin Zazzabin Lassa Nan Da 2030

Masana kimiyya a yankin yammacin Afirka sun ce ana iya samar da lasisin rigakafin cutar zazzabin Lassa kafin shekara ta 2030.

Sun bayyana hakan ne a lokacin da suke amsa tambayoyi manema labarai a yayin taron karawa juna sani na ‘Enable Lassa Program Workshop’ wanda kungiyar hadin gwiwa mai yaki da cututtuka (CEPI) da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) suka shirya a Abuja.

Binciken Enable, wanda hukumar CEPI ta ba da tallafin wajan gudanarwa, an yi shi ne don samar da kyakkyawar fahimta game da ainihin nauyin cutar zazzabin Lassa a yammacin Afirka, inda ake samun bullar cutar a kai a kai, da kuma jagorantar samar da alluran rigakafin cutar.

Kodinetar kungiyar Binciken na CEPI , Farfesa Bola Olayinka, ta ce suna fatan samun rigakafin cutar kafin shekarar 2030.

Inda ta kara da cewa, tuni aka samar da wasu masu neman alluran rigakafin, kuma kawai suna bukatar a yi gwaje-gwaje ne kan su, donmin duba ingancin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram