NDLEA Ta Damƙe Dagaci Da Wasu Mutum 11 Ɗauke Da Miyagun Ƙwayoyi A Sokoto

Jami’an hukumar hana sha da fatauci miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta yi nasarar cafke wasu mutane 11 a jihar Sokoto, da laifin Safarar miyagun kwayoyi.

Cikin mutane goma sha dayan, akwai Abubakar Ibrahim, mai unguwar Gidan Abba dake karamar hukumar Bodinga a jihar.

Hukumar ta samu mutanen da kunshin ranar Wiwi mai nauyin kilogiram 46, da magunan sanya maye, da kuma hodar iblis ta makudan kudade.

Daraktan yada labaran hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana hakan, a cikin wata Sanarwa daya rabawa manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Ya kara da cewa jami’an hukumar su a wani aikin hadin gwiwa da suka gudanar, a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Ikeja a Legas, sun samu nasarar cafke katan goma sha biyar na kwayar Tramadol.

Femi ya ce kwayoyin an shigo da su Najeriya ne daga kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa, da kuma Karachi, Pakistan.

An kuma kama wani mutum a filin jirgin saman jihar Enugu, bayan ya dawo daga Birnin Nairobi dake ƙasar Kenya, shima dauke da kayan maye.

Mutumin mai suna Madu Chukwuemeka yana dauke da wani sabulu dan kasar waje, sabulun da aka sarrafa shi ta hanyar amfani da Hodar Iblis, kuma yawansa ya kai Katan 76.

Ya ce suna ci gaba da bincike kan mutanen, suna kuma tattara bayanai zasu mika su gaba, don girbar hukunci daidai da Laifin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram