Amarya Ta Fasa Yin Auren Da Aka Ɗaura Wata Ɗaya, Ta Maida Akwatuna Da Sadaki

A yau Litinin Wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna, ta umurci wata matar aure, Maryam Dahiru da ta mayar da sadaki Naira 100,000 da akwatunan tufafin da ta karba daga hannun tsohon mijinta Salihu Yakubu.

Da yake yanke hukunci, alkalin kotun, Malam Rilwanu Kyaudai, ya tabbatar da rabuwar aure tsakanin ma’auratan ta hanyar Khul’i (saki ta hanyar yarjejeniya).

“Kawai za ta mayar da tufafin da bata ruga ta yi amfani da su ba, Mai karar ta kuma bukaci izinin Kotu da ta kwashe kayanta daga gidan tsohon mijin nata.” A cewar mai shari’an.

Tun da farko, Maryam Dahiru, ta bakin lauyanta Murtala Gyallesu, a ranar 12 ga watan Oktoba ne ta shigar da kara a gaban kotu inda take rokon kotu ta raba auren da suka yi wata daya ta hanyar Khul’i.

Ta ce yanzu ba ta da sha’awar auren, kuma a shirye take ta mayar da sadakin da ta karba domin a raba auren.

A nasa bangaren, Yakubu ta bakin lauyansa, M. M. Dahiru, ya ce yana son matarsa ​​kuma ba shi da niyyar sakin habibiyar tasa.

Yakubu ya roki kotu da ta umarci tsohuwar matarsa ​​da ta mayar da akwatunan auren da aka cika mata su da kayan da ya ba ta.

(NAN)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram