Adadin wadanda suka mutu sanadiyya ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa sakamakon guguwa mai karfi a kasar Philippines ya kai 98, yayin da wasu 63 suka bace, in ji hukumar kula bala’o’i tA kasar a ranar Litinin.
Hukumar ta kara da cewa mutane 69 ne suka jikkata sakamakon guguwar Nalgae mai zafi da ta afkawa kasar Philippines a karshen mako.
Sama da mutane miliyan 1.9 ne abin ya shafa, daga cikinsu 975,000 sun rasa matsugunansu.
Sama da 309,000 ne ke zama a wuraren da aka basu bayan kwashe su, in ji hukumar.
Shugaban kasar Ferdinand Marcos Jr ya ziyarci yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a lardin Cavite a ranar Litinin, inda ya kawo karin kayayyakin agaji.
Ya jadadda bukatar a kai dauki kafin guguwa domin tabbatar da tsaron mazauna yankin.
“Ayyukanmu na shawo kan ambaliyar ruwa sun kai gare su.
“Ruwa ya yi ta malalowa daga magudanar ruwa tare da mamaye garuruwa.
“Wannan shine dalilin da ya sa na ci gaba da tunatar da hukumomin rage haɗarin bala’i cewa abu mafi mahimmanci lokacin da muke shirye-shiryen rigakafin guguwa wanda shine magani.