Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadin nan ya ce matakin da babban bankin Kasa CBN ya dauka na kaddamar da sabbin tsare-tsare tare da maye gurbin wasu kudade na Naira ya samu goyon bayansa.
Gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele ya bayyana haka a ranar Larabar da ta gabata a Abuja inda ya bayyana cewa babban bankin zai fara raba sabbin takardun kudi na Naira 100, Naira 200, da Naira 500 da kuma Naira 1000 daga ranar 15 ga watan Disamba, bayan amincewar shugaban kasa.
Sai dai Ministar Kudi, Kasafi Tsare-tsare ta Kasa, Zainab Ahmed, a ranar Juma’ar da ta gabata, yayin zaman kare kasafin kudin shekarar 2023 da kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin kudi, ta mayarwa Emefiele martani a kan kudirin, inda ta ce CBN ba ta tuntubi ma’aikatarta ba kan shirin sake fasalin Naira da aka shirin yi, ba za ta iya yin tsokaci a kansa ba dangane da cancanta ko akasin haka.
Ministar ta ce, “Masu girma Sanatoci, CBN bai tuntubemu a ma’aikatar kudi game da shirin sake fasalin kudin Naira kuma ba za mu iya cewa komai dangane da cancanta ko akasin haka ba.
“Duk da haka a matsayin dan Najeriya mai fatan kasancewa a kan gaba a harkokin kasafin kudin, manufar da aka fitar a wannan lokaci tana nuna mummunan sakamako kan darajar Naira a kan sauran kudaden waje.
“Duk da haka, zan yi kira ga wannan kwamiti da ya gayyaci gwamnan CBN don yin bayani game da cancantar manufofin da aka tsara da kuma daidaito ko akasin haka na aiwatar da shi a yanzu.”
Sai dai a ranar Lahadin nan, Buhari, kamar yadda wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar, ya jaddada cewa yana goyon bayan matakin CBN na sake fasalin kudin Naira.