Dakarun Soji Sun Fatattaki Ƴan Ta’adda, Sun Hallaka Mutum Bakwai

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana a yau Lahadin cewa dakarunta sun kashe ‘yan ta’adda bakwai a karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna tare da kwato makamai.

Sanarwar da Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar, ta ce dakarun runduna ta 1 ta sojojin Najeriya da ke aiki da rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun kai farmakin share fage a yankunan Maidaro, Tudun Kagi, Kusharki da Anguwan Madaki na karamar hukumar.

Ya kara da cewa bayan kazamin fadan da yayi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda bakwai a wani samame daban-daban, har yanzu wasu ‘yan bindiga sun tsere daga farmakin na su.

Babban hafsan sojojin ya ce, a Maidaro, tudun Kagi, Kusharki da Anguwan Madaki, an kashe ‘yan ta’adda hudu, yayin da sojoji da ke yankin Sabon Birnin-Zartake, Ungwan Lima Riyawa da Tungan Madaki, suka kama wasu ‘yan bindiga da suka tsere daga tsaunin Kagi tare da kashe wasu guda uku.

Sanarwar ta kara da cewa, an samu nasarar kwato bindigogi kirar AK 47 guda biyu masu zagaye biyu na 7.62mm na musamman, bindiga mai sarrafa kanta guda daya mai dauke da harsashi uku, bindigogin dane guda shida, bindigogi kirar gida guda uku da kuma babura 4.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram