Hatsarin Mota Ya Ƙone Mutane 11 Ƙurmus A Enugu

A kalla fasinjoji 13 ne suka kone kurmus a wani mummunan hatsarin da ya afku a kusa da unguwar Four Corners a Enugu da misalin karfe 9 na daren ranar Lahadi.

Wata motar bas mai dauke da kujeru 14, wadda aka ce ta tahowa daga jihar Imo zuwa Adamawa, ta ci karo da tirela wanda ya jano ta kama wuta.

Dukkanin fasinjojin mutum guda daya ne ya tsira, fasinjojin an ce sun kone kurmus a hatsarin, wanda ya afku a karshen titin Enugu da Port Harcourt.

Wasu sun ce masu tausayi ne suka cece shi; wasu kuma suka ce ya fice daga motar ta taga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram