Masari Na Neman Afuwar Al’ummar Katsina

Gwamnan jahar Katsina da ke Arewa Maso Yammacin Najeriya, Aminu Masari ya ce yana roƙon afiwar al’ummar jahar.

Masari ya bayyana haka ne a yayin taron ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa da na gwamnan jahar.

Gwamnan ya ce da shi da sauran mutanen da suka jagoranci gwamnatinsa suna neman jama’a da su yafe ma su inda suka yi kuskure a yayin tafiyar da mulkin jahar.

Masari da ya ke tsokaci a game da matsalar tsaro a jahar, ya ce in an ce APC ce ta kawo rashin tsaro a Katsina to a jahar Sokoto fa da jam’iyyar PDP ke mulki ita kuma wa ya kawo ta?

Ya ƙara da cewa duk da matsalar tsaro to amma an samu ci gaba daga lokacin da APC ta amshi mulki zuwa yanzu, don haka ya kamata mutane su gode ma Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram