Na Tsani Aure A Rayuwa Ta – Cewar Matar Da Ta Kashe Mijinta Da Guba A Borno

Wata matar aure ‘yar shekara 25 mai suna Fatima Abubakar, wacce aka rawaito ta sheke mijinta, Goni Abbah da guba, ta ce ta aikata hakan ne saboda ta tsani aure.

Mamacin wanda shi ne babban Limamin yankin ya dawo daga masallacin ne a lokacin da wanda ake zargin wanda ita ce matar sa ta biyu ta cakuda guba a cikin abincinsa.

Da yake magana game da kama wanda ake zargin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Mista Abdu Umar, ya ce jami’an rundunar a Anguwan Doki sun kama wanda ake zargin ne a ranar 19 ga watan Oktoba.

CP Umar ya bayyana cewa a lokacin da Goni ya fara cin abincin da wanda ake zargin ta ba shi, sai lafiyarsa ta fara tabarbarewa, inda aka garzaya da shi asibitin kwararru na jihar inda aka ba shi kulawar gaggawa, abin takaici, daga baya ya rasu bayan sun dawo gida.

Umar ya ce an tura jami’an hukumar binciken manyan laifuka da leken asiri domin cafke wanda ake zargin bayan da iyalan mamacin suka kai rahoton faruwar lamarin a ofishin ‘yan sanda na GRA.

Ya ci gaba da cewa, da zuwan ‘yan sandan sun ga dimbin matasan unguwar da suka fusata, inda suka kai farmaki gidan wanda ake zargin domin kashe ta, amma ‘yan sandan sun yi nasarar shawo kan lamarin.

Ya kara da cewa, wacce ake zargin a cikin sanarwar ta, ta amsa laifin da ake zargin ta da shi, inda ta ce ta sayi gubar ne a kasuwar Monday Market a lokacin da ta riga ta yanke shawarar kashe shi.

Ya ce an rubuta karar a matsayin laifin kisan kai a ofishin daraktan kararrakin jama’a kafin a gurfanar da ita a gaban kotu.

Wanda ake zargin mai suna Fatima, wadda aka kama a hannun rundunar, ta ce ta kashe mijinta ne saboda ta gaji da auren.

Ta ce: “Ban taɓa son auren ba. Goni shine mijina na biyu; Na rabu da mijina na farko saboda na tsani aure.”

“A duk lokacin da na farka da cewa na yi aure, abin yana ba ni haushi. A wani lokaci sai na ruga wurin iyayena don neman a raba auren amma kullum sai su mayar da ni, suna neman na yi hakuri.”

“A wani lokaci, bayan wata biyu da na haifi ɗa na, sai na gudu na kwanta a wani gini da ba a kammala ba na kusan sati biyu, Daga baya na koma gidan mijina.”

“Ba wai bai yi min kyau ba, mu ba rigima muke yi ba. Mu biyu ne a gidan, ni ce matarsa ​​ta biyu kuma na aure shi tun shekarar 2021. Amma ni dai ina kyama idan kowane mutum ya zo kusa da ni.”

“Ban san abin da ke damuna ba. Ko yanzu da nake magana da ku, ban ji cewa ni ce wacce na kashe shi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram