Daya daga cikin Dattawan kasa kuma kwamishinan yada labarai a jamhuriya ta farko, Edwin Clark, a ranar Talata, ya caccaki shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan tafiyarsa zuwa birnin Landan na kasar Birtaniya.
Tafiyar dai ta kasance domin a duba lafiyarsa, ba tare da mika mulki ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ba.
“Ya kamata Buhari ya gaya wa ‘yan Najeriya ciwon da yake fama da shi”, in ji shi.
A cewarsa, ya kamata Buhari ya bi kundin tsarin mulkin kasa kuma ya yi abin da ake bukata kamar yadda ya dace a duniya, domin ba zai iya tafiyar da Najeriya daga kasashen waje ba.
Clark, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai a Abuja, ya ce a matsayinsa na shugaban kasa, ya kamata ya sanar da ‘yan Nijeriya duk irin ciwon da yake fama da shi.
Ya ce kamata ya yi a tunkari Kotun Koli don neman taswirar abin da Buhari ya ke yi ba tare da ya shaida wa ‘yan Nijeriya cikakkun bayanai kan halin da yake ciki ba.
“Najeriya ta mu ce gaba daya, Buhari yana daukar ‘yan Najeriya a wani matsayi na daban, wanda ba shi da ikon tashi zuwa Landan ba tare da mika mulki ga mataimakin shugaban kasa ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.” inji Clark