Na Kama Matata Tana Kwanciya Da Ɗan Uwana – Miji Ya Nemi Kotu Ta Raba Aure

Wani dan kasuwa mai suna Justine Onu, ya bukaci wata kotu a Abuja ta warware aurensa da matarsa Joyce, bayan da aikata wani laifi.

Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Onu ya bukaci warware auren nasu, bayan da ya kama matar sa na aikata lalata da dan’uwansa.

Ya bayyana kotun cewa ya gaza gane kan matar tasa tun ba yanzu ba, hakan ya sanya auren ya fice masa a rai kuma yake bukatar a kawo karshen auren.

Ya ce yanzu haka yana dauke da cutar hawan jini, sakamakon yawan samun matar sa da aikata abubuwan da basu kamata ba.

Ya ce a matsayin ta na matar gida baya iya kula da yaran da suka haifa, balle girki domin su ci, dama gazawar ta wajen sauke nauyin gida da ya rataya a wuyanta.

Sai dai da mai Shari’a ya juya ga wadda ake kara ta musanta dukkan laifukan, tana mai cewa bata aikata ba.

Alkaluma kotun mai Shari’a Labaran Gusau, ya dage sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Nuwamba, domin ci gaba da sauraron karar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram