Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa jarrabawar kammala karatun sakandare a Najeriya ta NECO, WAEC, NABTEBE, NBAIS, duk zasu kasance kyauta ne ga dalibai yan kasar.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a yau, yayin da yake bayyana kundin manufofin takararsa ta shugaban ƙasa (Blueprint) idan har yayi nasarar zama shugaban ƙasa a zaben 2023.
Kwankwaso yana taron ƙaddamar da jadawalin kundin manufofin takararsa a babban birnin tarayyar Abuja, inda yace za’a kara wa’adin jarabawar neman gurbin shiga jami’a ta JAMB zuwa shekaru hudu kafin ta daina aiki.