Ƴan Bindiga Sun Sace Ƙananan Yara 39 Cikin Gona A Katsina

Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.

Iyayen Yara talatin da tara da ƴan bindiga suka sace a yayin da suke aiki a gona a karamar hukumar Faskari dake jihar Katsina sun bukaci gwamnati data kawo masu dauki.

A cewar wata majiya yan bindiga a ranar Lahadi su da yawa sun sace yara a yayin da suke aiki a cikin gona.

A cewar majiyar kauyen Mairuwa anan ne abun yafi shafa. Ya bayyana cewar ƴan bindigar sun fara harbe-harbe a lokacin da suka zagaye Gonar.

Majiyar ta kara da cewa saida wakilan gonakin suka biya naira miliyan daya ga yan bindigar kuɗin haraji ga ƴan bindigar kafin su tattara yaran, inda Manya daga cikin su, sun tsere a lokacin harin.

Majiyar ta bayyana cewa sun bukaci naira miliyan ukku daga mai mallakin gonar domin ya samu damar girbe amfanin gonarsa ya kuma fara basu naira miliyan daya a cikin kudin da suka kayyade masa wanda daga baya ya fara aiki kafin ya cika musu kudin amma sai yan ta’addan suka ki yarda. A kauyenmu na Mairuwa kadai muna da Yara talatin da ukku daga cikin yaran da aka dauka tare da ƴan mata da suka isa Aure.

Ya kuma bayyana cewa mai mallakin gonar mazaunin Funtua ne amma yana da wakilai mazauna kauyen Mairuwa, inda ya bayyana cewa yan bindigar sunyi amfani da wayar daya daga cikin yaran da suka dauka gani da neman Miliyan 30 kuɗin fansa.

Ya kuma kara da cewa yan bindigar sunje gonar domin daukar mai gonar ko wakilansa sai suka ga basu same su ba sai suka yanke hukuncin daukar yaran.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda jihar Katsina SP Gambo Isah ya bada tabbacin cewa jami’an yan sanda da sauran hukumomin tsaro da Gwamnati domin ceto yaran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram