EFCC Ta Yi Shigar Bazata Kasuwar Canjin Ta Kano, Ta Kama Wasu Jami’ai

Akalla masu hada-hadar canji kudade BDC guda Takwas ne aka kama bayan wani sumame da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta kai a kasuwar Wapa ta Kano.

Jarodar Daily Trust ta tattaro cewa jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano sun kai farmaki kasuwar forex a yammacin ranar Talata da motoci kusan takwas da kuma jami’ai dauke da muggan makamai, lamarin da ya jefa kasuwar cikin wani yanayi.

Hakan ya biyo bayan da ‘yan kasuwa a Kano suka ce sun samu labarin cewa tun da farko hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kai farmaki ga abokan aikinsu a Abuja inda ta cafke wasu dangane da karin dala da aka yi kwanan nan a kasuwannin bayan fage.

Daya daga cikin ‘yan kasuwar da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce kafin jami’an EFCC su kai farmaki kasuwar da yammacin ranar Talata, wasu abokan aikinsa sun rufe shagunansu a wani bangare saboda labarin da aka samu a Abuja, kuma a lokacin da jami’an hukumar suka mamaye kasuwar daga cikinsu sun rufe da sauri suka fice daga kasuwa.

Wani dan kasuwar ya ce saboda ci gaban da aka samu ya sa da yawa daga cikinsu sun yanke shawarar barin kasuwar na wani dan lokaci har sai abin da hali yayi, inda ya ce ba wannan ne karon farko da EFCC ke kai sumame kasuwar ba.

“Duk lokacin da suka kai farmaki wannan kasuwa, farashin dala zai tashi. Misali, a yau (Laraba) dala ta kai Naira 845 sabanin Naira 835 da ake sayar da ita jiya (Talata) kafin EFCC ta kai sumame.

“A gaskiya a makon da ya gabata muna sayar da shi a kan Naira 750 amma kafin karshen makon ta haura Naira780. Matsalar ita ce saboda gwamnati ba ta sakin dala. Lamarinba laifinmu bane. Muna siya da tsada, don haka dole mu sayar da shi ta hanyar da za mu samu riba kadan,” in ji dan kasuwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram