Gwamna Zulum Ya Ɗauki Nauyin Karatun Marayu 300

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Talata ya kaddamar da shirin bayar da tallafin karatu na Naira miliyan 300 domin tallafa wa marayu 300 da iyayensu suka mutu a matsayin masu aikin sa kai da ’yan banga da mafarauta karkadhin kungiyar ‘Civilian Joint Task Force (CJTF)’.

Masu aikin sa kai na da hannu wajen yakar ‘yan Boko Haram da ISWAP tare da sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro a jihar Borno.

Zulum a wajen kaddamar da taron wanda aka gudanar a dakin taro na Multi-purpose House dake Maiduguri, ya ce Naira miliyan 300 za ta biya duk wani bukata a fannin ilimi na marayu 300 a duk matakin karatunsu na farko, kafin a ci gaba da tallafa musu a nan gaba.

Idan ba’amanta ba, Gwamnan a yayin gabatar da kasafin kudin shekarar 2020 ya yi alkawarin tallafa wa marayu a karkashin shirin tallafawa iyalan wadanda suka sadaukar da rayuwansu ga jihar Borno.

Baya ga tallafin, Zulum ya kuma amince da tallafin akalla Naira Milliyan 15 ga iyaye mata da sauran masu kula da marayu 300n.

Kowacce daga cikin iyaye mata ko masu kula da marayun sun sami Naira 50,000 tare da buhun shinkafa, buhun masara da kayan sawa.

A jawabansu daban daban, shugaban kwamitin da Zulum ya kafa domin zakulo marayu 300n, Barista Kaka Shehu Lawan da kwamandan Operation Hadin Kai, Manjo Janar Christopher Musa, sun yaba da shirin gwamnan na jihar Borno.

Haka kuma a yayin kaddamar da tallafin karatu a ranar Talata ga marayu 300 na masu aikin sa kai da aka kashe, Zulum ya sanar da karin kashi 35 cikin 100 na alawus-alawus da ake biyan masu aikin sa kai duk wata.

Ya kara da cewa, An kara alawus din ne daga Naira 20,000 zuwa Naira 30,000 duk wata

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram