PDP Ta Shiga Ruɗani, Ta Kori Ɗan Takarar Ta Na Gwamna Da Wasu Jiga-jigan Jam’iyya

PDP Ta Shiga Ruɗani, Ta Kori Ɗan Takarar Ta Na Gwamna Da Wasu Jiga-jigan Jam’iyya

Jam’iyyar PDP ta kori daya daga cikin ‘yan takararta na gwamna a jihar Ogun, Mista Jimi Lawal.

An kori Lawal ne tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar da aka dakatar tun da farko saboda shirya zaben fidda gwani ba bisa ka’ida ba.

Sauran wadanda aka kora daga jam’iyyar sun hada da Shugaban Ijebu Arewa maso Gabas, Aremo Tope Ashiru; Ademola Ojoye; Madam Fatima Sobanire; Mrs Adenike Asorona; Muyiwa Odebiyi da kuma Moruf Olajide.

Sakataren kudi na jam’iyyar PDP na jihar, Bola Odumosu, wanda aka zarge shi da rubuta wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) wasika a Ogun, inda ya nemi ta halarci zaben fidda gwanin da aka yi.

Haka kuma an dakatar da Fasiu Ajadi da Kola Akinyemi wadanda talakawan jam’iyyar ne na tsawon watanni shida.

An dauki matakin ne a taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar PDP na jihar Ogun da aka gudanar a ranar Talata a sakatariyar jam’iyyar da ke Abeokuta.

A taron da shugaban kungiyar, Sikirulahi Ogundele ya jagoranta, an amince da shawarwarin kwamitin ladabtarwa da jam’iyyar ta kafa, wanda ya kai ga korar Lawal da sauran su.

Tun da farko, Shugaban kwamitin ladabtarwa, Barista Tola Odulaja, yayin da yake gabatar da rahotonsa, ya ce an samu ‘ya’yan jam’iyyar da aikata muguwar dabi’a, da suka hada da cin mutunci, aiki da dabi’un da za su iya kawo wa PDP suna, wakilci na yaudara, jabun takardu, sa hannun jami’an jam’iyyar, nuna rashin biyayya ga umarnin kwamitin ayyuka na jam’iyyar na kasa ta hanyar gudanar da babban taron jiha.

Shugaban kwamitin ya ce mambobin da suka yi kuskure lokacin da aka gayyace su ta hanyoyi daban-daban sun ki bayyana gaban kwamitin.

“Mun kai musu wasiƙu da kanmu. An tursasa wasu daga cikin wadanda suka je kai wasikun, A gaskiya sun ki amsa tuhumar da ake yi musu,” in ji Odulaja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram