Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya dakatar da rade-radin cewa yana aiki tare da gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP.
Ana zargin Peter ne a baya da hada kai da gwamnonin domin lashe zaben shugaban kasa a 2023.
Idan zaku iya tunawa cewa Obi ya sha ganawa da Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe, Nyesom Wike na jihar Ribas, Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu, da Seyi Makinde na jihar Oyo.
Wadanda suka fafata da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.
Tarurrukan dai sun kara ruruta wutar rade-radin cewa gwamnonin za su yi kokarin ganin sun kai tsohon gwamnan jihar Anambra a zaben watan Fabrairu mai zuwa.
Amma da yake magana a Makurdi, babban birnin jihar Binuwai yayin wata ziyara da ya kai wa Gwamna Ortom a ranar Talata, ya ce shi da gwamnonin PDP na da buri daya na samar da ingantacciyar Najeriya.
Obi ya caccaki gwamnatin APC kan rashin shugabanci a lokacin da ake fama da tabarbarewar tattalin arziki da al’amuran jin kai da suka addabi al’ummar kasar nan.