Rundunar Ƴan Sanda Ta Ƙaryata Batun Kai Hari Ta’addanci A Cikin Birnin Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta karyata labarin wani harin ta’addanci da aka kai a wata al’umma a Kano a matsayin na karya a ranar Laraba, 2 ga Nuwamban shekarar 2022.

DAILY POST ta ruwaito cewa labarin harin ta’addanci ya samo asali ne daga wani rahoto ta yanar gizo.

Sai dai wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna ya fitar, ya ce babu wani harin ta’addanci da aka kai.

Haruna, wanda ya bayyana labarin a matsayin wanda ba gaskiya ba ne, kuma wanda baida tuce balantana makama, , ya danganta lamarin ga marubutan da ke son kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake samu a jihar a halin yanzu.

SP Haruna ya umarci mazauna Kano da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na yau da kullum ba tare da fargaba ba, inda ya ce tuni rundunar ta tsara dabarun tabbatar da tsaro a fadin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram