Wata Mace Ta Nemi Kotu Ta Tilastawa Minjin Ta Biyan Ta Dubu 30,000 Duk Wata

Wata mata mai juna biyu, Ummulkhairi Salisu, a ranar Talata, ta yi roko ga wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a Magajin Gari, a jihar Kaduna, da ta umurci tsohon mijinta, Hassan Malam da ya biya ta naira 30,000 duk wata a matsayin alawus na kulawa da raino.

Mai karar, ta bakin lauyanta, Malam N.T. Abdullahi, ya kuma roki kotun da ta tabbatar da sakin aure daya da wanda ake kara ya bayar.

Abdullahi ya ce, “Muna kuma rokon kotu da ta bai wa mai karan izinin kwashe kayanta da akwatunan lefenta daga gidan wanda ake kara.”

A nasa bangaren, wanda ake kara ta bakin lauyansa, Sadik Marafa, ya ce ya yanke hukuncin saki ne kan wanda ya kai karar saboda ta bar gidan aurensu ba tare da saninsa ba.

Marafa ya ce, “Wanda nake karewa yana sane da cewa tana da ciki wata biyar kuma Naira 2,000 kawai zai iya biya a matsayin alawus na rmshayarwa mai makon Naira 30,000 da take nema.

“Za mu biya kudin magunguna, mu sayo tufafin jarirai da zaran ta haihu.”

Ya bayyana cewa bai san wani kayan daki na mai karar ba, ya kara da cewa ba ta zo da komai gidansa ba lokacin da ya aure ta.

Alkalin kotun, Malam Rilwanu Kyaudai, ya dage sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba (NAN) Daily Trust.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram