Ni Zan Yi Sulhu Da Ktungiyar IPOB Idan Na Zama Shugaban Ƙasa —Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar LP, Peter Obi ya ce zai yi sulhu da haramtacciyar kungiyar IPOB mai neman ballewa daga Najeriya da sauransu, idan ya ci zabe a 2023.

Peter ya bayyana cewa idan ya ci zabe, kamun ludayin gwamnatinsa zai kasance da tattauna da duk wata kungiya ko bangarori masu korafi ko matsala da gwamanti domin yin sulhu da samun daidaito.

Ya sanar da haka ne a hirar da aka yi da shi kan sha’anin tsaron Najeriya a hedikwatar Rukunin Kamfanin Yada Labarai na Media Trust masu jaridar Daily Trust da Aminiy da kuma Trust TV a Abuja.

A cewarsa, “Na sha fada, Najeriya ba ta kai kasar Brazil yawan masu korfai ba; Idan kuna so zan bayyana muku kasashen da a baya suka yi fama daga irin wadannan korafe-korafe, kama da Brazil zuwa Meziko da sauransu.

“A yankin Kudu maso Gabas, sulhu zan yi da su, mu tattauna tun da dimokuradiyya ce kuma a dimokurasiyya za a iya shugabanci ta hanyar sulhu.

“Idan da wanda bai ji dadin abin da aka yi ba ba, sai ka kira shi ku zauna ku tattauan.

“Ko a gidana matata da ’ya’yana sukan yi korafi. Duk wanda ya ce tun da suke tare da matarsa ba su taba samun sabani ba, to sai dai idan ba aure suke yi ba. Akan samu sabani, sannan a sasanta — wannan shi ne korafi.”

IPOB haramtacciyar kungiya ce mai rajin ballewa daga Najeriya da kuma kafa kasar Biyafara — wadda za ta kunshi Kudu maso Gabas da kuma Kudu maso Kudu na Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram