Yadda Wani Bugaggen Kofur Ya Kaɗe Janar Ɗin Soja Da Mota Ya Rasu A Legas

Yadda Wani Bugaggen Kofur Ya Kaɗe Janar Ɗin Soja Da Mota Ya Rasu A Legas

Wani Kofur na sojin ƙasa, Abayomi Ebun, ya murkushe daraktan kuɗi na cibiyar sake tsugunar wa ta sojojin Nijeriya, NAFRC, A. O James da mota a jihar Legas.

PRNigeria ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Ebun, wanda ke aiki a cibiyar samar da albarkatu ta sojin Nijeriya, NARC, ke fito wa da mota daga tsohon barikin NAFRC da ke Legas.

PRNigeria ta tattaro cewa shi marigayin na tafiya gidansa ne da ke cikin barikin, sai motar sojan ta buge shi daga baya.

Nan da nan bayan faruwar lamarin, a yi gaggawar kai babban jami’in sojan zuwa cibiyar kula da lafiya ta NAFRC, inda likitocin cibiyar suka tabbatar da rasuwarsa.

Wata majiya a barikin na NAFRC ta shaida wa PRNigeria cewa Ebun ya bugu ne a lokacin da lamarin ya faru kuma yana tukin ganganci.

“Hukumar NAFRC ta tsare shi don ci gaba da bincike,” in ji majiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram