Wani Mutum Ya Hallaka Ƙaramin Yaro Bayan Lalata Da Shi

Rundunar yan sanda jihar Ogun ta bayyana cewa ta kama wani mutum dan kimanin shekaru talatin da shidda mai suna Sikiru Ajibola wanda ake zargin da lalata da wani yaro mai shekaru biyar wanda har yayi sanadiyyar mutuwarsa a kauyen Ogijo dake karamar hukumar Sagamu dake jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda jihar SP Abimbola Oyeyemi ya bayyana hakan a ranar Asabar cikin wata takarda a Abeokuta.

Oyeyemi ya bayyana cewa ankama Wanda ake zargin a ranar Juma’a biyo bayan rahoto da shugaban kungiyar Cigaban Al’ummar yankin Olorunwa Arogbeja Ogijo ya kai a shelkwatar hukumar yan sandan yankin.

Oyeyemi ya bayyana cewa shugaban kungiyar ya bayar da rahoton cewa wani daga cikin mazauna yankin ya sanar dashi cewa Wanda ake zargin ya aikata laifin lalata da yaro, wanda a sanadiyyar haka ya mutu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda jihar ya kara da cewa bayan samun rahoton shugaban hukumar yan sandan yankin na Ogijo Enatufe Omoh ya hanzarta tattara jami’ansa domin zuwa wurin da lamarin ya faru inda aka kama wanda ake zargin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram