Kisan Uromi: Gwamnatin Kano ta bai wa iyalan mafarautan da aka kashe a jihar Edo tallafin dubu 300 kowannen su

Shekara guda bayan kisan mafarauta ƴan asalin jihar Kano a garin Uromi, na jihar Edo, Gwamnatin Jihar Kano ta cika alkawarin da ta dauka na tallafa wa iyalan wadanda aka kashe da kuma wadanda suka tsira daga harin da ya afku, inda ta raba musu kudade da kayan abinci.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin ziyarar da ya kai karamar hukumar Bunkure, inda aka tara iyalan wadanda abin ya shafa.

Ya ce matakin ya biyo bayan umarnin gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, bayan an gano cewa alkawarin da aka yi a baya lokacin ziyarar jaje ba a cika ba.

A cewarsa, iyalai 16 na wadanda aka kashe sun karbi Naira 300,000 kowanne, yayin da wadanda suka tsira daga harin suka samu Naira 200,000 kowannensu, tare da buhunan shinkafa guda biyu ga kowanne su.

Waiya ya tuna cewa gwamnan Kano tare da takwaransa na Jihar Edo sun kai ziyara domin jajanta wa al’ummar yankin bayan harin da ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 19, yayin da wasu 13 suka tsira daga harin da aka kai musu yayin tafiya.

Ya kara da cewa duk da cewa Gwamnatin Kano ta cika nata bangaren, Gwamnatin Jihar Edo ma ta yi alkawarin cewa za ta biya diyya ga wadanda abin ya shafa nan ba da jimawa ba.

“An riga an bude asusun banki ga iyalan, kuma muna sa ran gwamnatin Edo za ta fitar da kudaden a kowane lokaci,” in ji shi.

Kwamishinan ya bukaci iyalan da su ci gaba da hakuri, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnatocin jihohin biyu na da kudurin tabbatar da adalci da tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Ya bayyana lamarin a matsayin “babbar masifa ta kasa,” tare da mika sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan, yana kuma addu’ar Allah ya jikansu.

Hakazalika, ya ce kwamitin da Gwamnatin Kano ta kafa karkashin jagorancin mataimakin gwamna ya tuntubi hukumomi a Jihar Edo domin tabbatar da an bi hanyoyin da suka dace wajen magance lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *