Kungiyar Izala a Katsina ta yi wa Sheikh Yakub Yahya ta’aziyyar rasuwar dansa

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’iqamatis Sunnah, JIBWIS, reshen jihar Katsina, ta kai ziyarar ta’aziyya ga Sheikh Yakub Yahya Katsina, bisa rasuwar ɗansa, Sheikh Ammar.

Tawagar ta kai ziyarar ne a ranar Litinin, 5 ga Oktoba, 2026, a gidan Sheikh Yakub Yahya da ke yankin Kofar Kaura, cikin birnin Katsina.

Tawagar JIBWIS ta jihar Katsina ta je ta’aziyyar ne, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na jihar, Sheikh Dr. Yakubu Musa Hassan Katsina, wanda aka fi sani da Sautus-Sunnah.

Tare da shi akwai wasu daga cikin muƙarabban ƙungiyar, ciki har da mai magana da yawun ƙungiyar.

Haka kuma, tawagar ta ƙunshi shugaban masu wa’azi da shugaban masu da’awa, da wasu daga cikin ’yan agaji na ƙungiyar, da sauran jami’an JIBWIS.

Da yake isar da saƙon ta’aziyyar, Sheikh Dr. Yakubu Musa Hassan Katsina ya ce ya zo ne a madadin ƙungiyar JIBWIS ta jihar Katsina baki ɗaya.

Ya bayyana rasuwar Sheikh Ammar a matsayin babban rashi, tare da miƙa ta’aziyya ga Sheikh Yakub Yahya da iyalansa.

Sheikh Yakubu Musa Hassan ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da Ya jiƙan marigayin, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sa Aljanna ce makomarsa.

Haka kuma, ya roƙi Allah Ya bai wa iyayen marigayin, ’yan uwansa da sauran al’umma hakurin jure wannan babban rashi.

Tawagar ta kuma yi addu’a ga Allah Ya bai wa iyalan Sheikh Yakub Yahya ƙarfin zuciya da haƙurin jure rashinsa.

JIBWIS ta Katsina ta bayyana irin wannan ziyara a matsayin wani ɓangare na nuna goyon baya da tausayi ga iyalan mamaci a lokacin da suke cikin juyayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *