Masu yi wa Atiku Abubakar kamfen a matakin kananan hukumomi sun gudanar da taron farko a Katsina

 

Masu yi wa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar kamfen a ƙananan hukumomi 34 na Jihar Katsina, domin zaɓensa a 2027, sun gudanar da taronsu na farko a ranar Talata, 25 ga Agusta, 2026, a ofishin kamfen ɗin ɗan takarar gwamnan jihar, Sanata Ahmad Babba Kaita, da ke Katsina.

Taron, wanda ya samu halartar wakilan dukkan ƙananan hukumomin jihar, ya tattauna dabarun da za a bi domin ganin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta samu nasara a zaɓen 2027. An kuma buƙaci mahalarta su tabbatar da cewa kamfen ɗin ya gudana cikin lumana, tare da kiyaye dokokin INEC da ƙa’idojin tsaro.

Kodinetan kamfen ɗin Atiku Abubakar na Jihar Katsina, Alhaji Surajo Aminu-Makera, ya ce yana da cikakken yakinin cewa ADC ta yi zaɓi mai kyau wajen tsayar da Alhaji Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa, da kuma Sanata Ahmad Babba Kaita a matsayin ɗan takarar gwamnan Katsina, yana mai cewa ƙwarewa, gogewa da farin jinin ’yan takarar na daga cikin abubuwan da za su taimaka wajen samun nasara.

Ya umarci kodinetocin ƙananan hukumomi da su gudanar da shawarwari cikin kwanaki 10 domin zaɓar kodinetocin mazabu, yayin da su kuma zaɓi kodinetocin rumfunan zaɓe cikin gaggawa. Ya jaddada cewa zaɓen jami’an kamfen ɗin ya kasance bisa amana, jajircewa da kuma tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a ƙananan hukumomin da abin ya shafa.

A cewar Abubakar Ahmed, Mai Magana da Yawun Kamfen ɗin Ɗan Takarar Gwamnan Katsina, Sanata Ahmad Babba Kaita, taron ya kuma samar da ingantacciyar hanyar sadarwa tsakanin mambobin kamfen, yayin da aka tabbatar da cewa ƙofofin jagorancin kamfen za su kasance a buɗe domin karɓar shawarwari da sauraron matsalolin da ka iya tasowa yayin gudanar da kamfen ɗin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *