Daga Lawal Gwanda
An kammala wani taron horas da kara wa juna ilimi na tsawon kwanaki biyu, wanda aka shirya domin Sakatarorin Kananan Hukumomi 34 na Jihar Katsina, a birnin Kano.
Taken taron shi ne: “Karfafa Jagoranci na Gudanarwa da Inganta Tasirin Cibiyoyin
Gudanar da Ayyukan Kananan Hukumomi a Jihar Katsina.”
Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu ta Jihar Katsina ce ta shirya tare da gudanar da taron, cikin hadin gwiwa da kamfanin Kado Generation Integrated Services Limited.
An gudanar da taron daga ranar 22 zuwa 23 ga watan Agustan 2026, da nufin bunkasa tsarin gudanar da harkokin kananan hukumomi a jihar.
Taron ya taimaka wajen kara wa mahalartan ilimi da fahimta kan hanyoyin gudanar da ayyukan sassan da suke jagoranta a matsayin Sakatarorin Kananan Hukumomi.
Wannan ne karo na farko da aka shirya irin wannan horaswa a jihar.
A jawabinsa, Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Honarabul Bishir Tanimu, ya bayyana taron a matsayin muhimmiyar kafa da za ta taimaka wajen bai wa Sakatarorin Kananan Hukumomi kwarewar da ake bukata domin inganta yadda suke gudanar da ayyukansu.
Honarabul Bishir Tanimu ya bukaci mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar da cewa wadanda suke karkashinsu ma sun amfana da wannan ilimi, domin bunkasa tsarin gudanar da kananan hukumomi.
Ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, bisa damar da ya bai wa ma’aikatar wajen sake fasalin tsarin gudanar da harkokin kananan hukumomi a jihar.
Shi ma babban mai gabatar da horon daga kamfanin Kado Generation Integrated Services Limited, Alhaji Gambo Abdullahi, ya bayyana cewa mahalartan sun samu dimbin ilimi daga cikin shirin.
Ya ce ilimin da suka samu zai taimaka musu wajen gudanar da harkokin kananan hukumominsu cikin sauki da inganci.
Alhaji Gambo Abdullahi ya kara da cewa, ba kowace gwamnatin jiha ce ke da irin wannan jajircewa da damuwa wajen daukar nauyin shirya irin wannan horo ga ma’aikatanta ba.
Ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Katsina da Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu bisa damar da suka bai wa kamfaninsu na gudanar da wannan shiri cikin nasara.
Daga cikin manyan jami’an ma’aikatar da suka taimaka wa Kwamishinan wajen ganin shirin ya yi nasara akwai Daraktan Gudanarwa da Samar da Kayayyaki, Alhaji Bello Isah Fago; Daraktan Ayyukan Gama-gari, Alhaji Halliru Abdullahi; da Daraktan Siyasa, Alhaji Sa’adu Abdullahi.
