Daga Lawal Gwanda
Mai ba Gwamnan Jihar Katsina shawara kan Hukumar Binciken Kananan Hukumomi, Hon. Lawal Rufa’i Safana, ya bayyana damuwa kan rashin kyakkyawan tsarin ajiye bayanai da kuma raunin kulawa da ayyuka da Shugabannin Ma’aikata (HOPs) ke yi a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar.
Hon. Lawal Rufa’i ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata ganawa da dukkan Shugabannin Sassan Ma’aikata, wadda aka gudanar a zauren taro na Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta ta Jihar Katsina.
Mai ba Gwamnan shawarar ya zargi HOPs da gaza sa ido da kuma kulawa yadda ya kamata kan ayyukan sauran sassan gudanar da aiki a kananan hukumomin da suke jagoranta.
Ya kuma umarce su da su tabbatar da an rubuta, tattara tare da adana dukkan muhimman bayanai da suka shafi gudanar da harkokin kananan hukumomi yadda ya kamata.

Ya ce: “Dole ne a tabbatar da cewa wadannan takardu suna cikin fayilolinku yadda ya kamata. Bayanan dole su kasance tare da ku, domin idan aka bukace su, ku ne za a tambaya, kuma dole ne ku iya gabatar da su.”
Hon. Lawal Rufa’i ya kuma nuna damuwa kan rashin cikakken bayani da alhaki game da saye da rabon motocin Kansiloli a kananan hukumomi.
Ya ce: “Wani batu da ya ja hankalina sosai shi ne batun motocin Kansiloli. Na fahimci cewa a wasu lokuta, an ba su kudin motocin ne domin su je su saya. A wasu lokutan kuma, an sayi motocin, amma babu wani bayani da ke nuna cewa an yi amfani da kudin gwamnati wajen sayen mota ga wani mutum, nawa aka saye ta, wane irin mota ce, wane launi take da shi, lambar chassis, lambar rajista, da kuma wanda aka ba ta.”
Yayin da yake ba HOPs shawarar su sanya ido kan ma’aikatan da ke sayar da kadarorin gwamnati ba bisa ka’ida ba, Hon. Lawal Rufa’i ya tabbatar musu da cewa za a samar musu da yanayi mai kyau da zai ba su damar gudanar da ayyukan da aka dora musu. Ya kuma jaddada cewa dole ne su tabbatar da an kafa da’a da ladabtarwa tsakanin ma’aikata.
A nasa jawabin, wakilin Daraktocin Taro na Harkokin Gudanarwa da Kudi, Alhaji Salisu Usman Dangamau, ya tabbatar wa Mai ba Gwamnan shawarar goyon bayansu ga sassan ma’aikata wajen tabbatar da ingantaccen tsarin adana bayanai.
Haka kuma, Shugaban Daraktocin Taro na Ma’aikata, Alhaji Sam’ila Bala, ya gode wa Mai ba Gwamnan shawarar, tare da tabbatar masa da cewa a shirye suke su gudanar da ayyukansu yadda ake bukata, kuma bisa umarnin gwamnati.
Kyakkyawan tsarin adana bayanai da kuma ladabtarwa na daga cikin muhimman abubuwan da za su taimaka wajen inganta gaskiya, rikon amana da ingancin aiki, bisa hangen nesan gwamnatin Gwamna Dikko Umaru Radda.



