Jaruman Ma’aikatar Nollywood Da Aka Sace Sun Shaƙi Iskar Ƴanci

Jaruman Ma’aikatar Nollywood Da Aka Sace Sun Shaƙi Iskar Ƴanci

Taurarin fina-finan Najeriya biyu, Cynthia Okereke da Clemson Cornel Agbogidi da aka sace kwanaki shida da suka gabata sun sami ‘yanci.

An yi garkuwa da jaruman fim din ne bayan da suke daukar wani fim a garin Ozalla da ke Enugu.

Da take tabbatar da sakin su daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su, Daraktar Sadarwar Jaruman Sadarwa ta Najeriya, Monalisa Chinda Coker ta wata sanarwa da ta fitar ta ce, “Muna farincikin sanar da jama’a cewa an sako ‘yan fim din da aka yi garkuwa da su Cynthia Okereke da Clemson Cornel Agbogidi ba tare da wani rauni ba.

Shima Shugaban kungiyar ‘yan wasan kwaikwayo ta Najeriya, Ejezie Emeka Rollas, ya sanar da sakin su daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su, inda ya ce, Allah ya sa su ‘yantar da su ba tare da sun ji rauni ba.

Ya wallafa cewa, “A madadin iyalansu, shugaban ya nuna matukar jin dadinmu ga masana’antar Nollywood da ‘yan Najeriya baki daya bisa goyon baya da addu’o’i a lokacin da aka sace su.

Ya bukaci ’yan uwa da su kasance masu lura da tsaro a yayin da suke bakin aiki wajan daukar shirin fim, kuma su rika daukar matakan kariiya kan tsaron lafiyarsu a kowane lokaci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *