Wani Mutum Ya Kashe Ƙaninsa Saboda Waya A Nasarawa
A yammacin ranar Talata ne wani mutum mai suna Ibrahim Musa ya daba wa wani dan uwansa mai suna Muhammad Musa mai shekaru 15 wuka ta hanyar da bacewar wayarsa a garin Mararaba da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa.
Wani shaida mai suna Babatunde Idowu, ya ce Ibrahim yana kokawa ne don karbo wayar daga hannun Muhammad wanda ya zarga da sata da kuma boye ta.
Shaidan ya ce, “A lokacin da Ibrahim ke matsa wa marigayi Muhammad lamba don ya amshi bwayar da karfi, sai ya zaro wukar daga aljihunsa ya daba masa a kirji sannan Muhammad ya fadi kasa warwas
“Da sanin cewa Muhammad ya mutu ne, sai Ibrahim ya jefa wukar a cikin wata magudanar ruwa, ya gudu daga wurin.
“Duk da haka, wasu matasa sun bi shi suka kama shi kafin su mika shi ga ‘yan sanda.”
Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaiito cewa tuni aka binne gawar Muhammad kamar yadda addinin Musulunci ya tanada
