Jagoran Yarabawa, Gani Adams, ya koka da cewa an mayar da rundunar tsaron Amotekun Corps ta Kudu maso Yamma ta Najeriya kayan siyasa, yana mai cewa rashin tsaro a kasar ya koma tamkar kasuwanci kamar yadda jaridar PUNCH ta rawaito.
Adams ya bayyana hakan ne a wata hira, inda ya bukaci gwamnatin tarayya ta amince da kafa ‘yansandan jihohi domin magance matsalar tsaro da ke kara ta’azzara.
Ya ce tsarin tsaron da ke hannun gwamnati kadai ba zai wadatar ba, yana mai jaddada bukatar hadin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma.
Ya kuma zargi yadda ake daukar ma’aikata cikin ƙungiyar tsaro ta Amotekun da siyasa, yana mai cewa wasu shugabanni na amfani da shi wajen bai wa mabiyansu aiki maimakon la’akari da kwarewa.
Haka zalika, ya nuna damuwa kan kashe-kashen sarakuna a yankin Kudu maso Yamma, inda ya ce akalla sarakuna bakwai sun rasa rayukansu, yayin da satar mutane da sauran laifuka ke kara yaduwa har zuwa manyan birane.
Adams ya gargadi cewa idan ba a dauki matakan gaggawa ba, matsalar tsaro za ta kara muni kafin zabukan 2027, yana mai jaddada cewa kafa ‘yan sandan jihohi da karfafa bayanan sirri a matakin al’umma ne mafita mafi inganci.
