NAWOJ da KATDICT za su horas da Mata Yan jarida kan fasahar zamani a Katsina.

Ƙungiyar ’Yan Jarida Mata ta Najeriya, NAWOJ, reshen Jihar Katsina, ta nemi haɗin gwiwa da Hukumar Fasahar Bayanai da Sadarwa ta Jihar Katsina, KATDICT, domin ƙarfafa ƙwarewar mata ’yan jarida a fannin fasahar zamani, basirar wucin-gadi, AI, tsaron yanar gizo da kuma amfani da kafafen sada zumunta.

Darakta-Janar na KATDICT, Naufal Ahmad, ya marabci wannan yunƙuri, tare da tabbatar wa NAWOJ cewa hukumar a shirye take ta tallafa wa ƙungiyar ta hanyar shirye-shiryen horaswa da bunƙasa ƙwarewa. Ya kuma buƙaci ’yan jaridar da suka amfana da irin waɗannan horaswa su riƙa isar da ilimin da suka samu ga sauran mambobin ƙungiyar.

Ahmad ya nuna damuwa kan yaɗuwar labaran ƙarya da bayanan yaudara, musamman ganin yadda ake ƙara amfani da fasahar AI wajen ƙirƙirar ko sauya hotuna, bidiyoyi da sauran abubuwan da za su iya yaudarar jama’a. Ya buƙaci ’yan jarida su ƙara ƙwarewa wajen tantance sahihancin bayanai tare da kiyaye ƙa’idojin aikin jarida.

Shugabar NAWOJ reshen Katsina, Hajiya Fatima Sanda Kaita, ta ce ƙungiyar na neman horaswa kan yadda za a yi amfani da AI wajen aikin jarida, ciki har da bincike, sauya sauti zuwa rubutu, fassara, samar da abun ciki da kuma tantance sahihancin bayanai. Ta kuma nemi horas da mambobin ƙungiyar kan gudanar da kafafen sada zumunta da kuma samar da labarai ta hanyoyin zamani.

A cewar Sakatariyar NAWOJ reshen Jihar Katsina, Faith Awa Maji, wadda ta fitar da sanarwar, ƙungiyoyin biyu sun amince su yi aiki ta hannun jami’an da za a ɗora wa alhakin hakan domin tsara taswirar haɗin gwiwar da kuma gano muhimman shirye-shiryen da za a fara aiwatarwa. Ta ce haɗin gwiwar zai samar da damammaki masu ɗorewa ga mata ’yan jarida wajen inganta ƙwarewarsu ta zamani, tsaron yanar gizo da kuma kwarewa a aikin jarida na.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *