Daga Wakiliyarmu Amira Salisu Batsari.
Gwamnatin Jahar Niger a jiya ta sanar da cewa jami’an tsaro, sun ceto Manoma 22 da Akayi garkuwa dasu a ranar Juma’a a ƙauyen Kuchi dake karamar hukumar Munya .
Kwamishinan Kula da Harkokin Tsaron Cikin Gida da Jinƙan Al’umma Emmanuel Umar , ya sanar da hakan a cikin wata takarda, ya kuma bayyanar da cewa, daga cikin wadanda aka kubutar harda kananan yara.
Ya bayyana cewa, an ceto mutanen bayan da jami’an tsaro suka shiga cikin dajin, inda suka yi musayar wuta da Yan ta’addan tare da harbe harbe.
” Lokacin musayar wutan, Ƴan Ta’addan sun ruga inda suka buya a daji tare da barin wadanda suka kama da sauran kayayyakinsu.” Ya fada
Umar ya bayyana cewa, mutanen an mayar dasu ga iyalansu.
Yace daya daga cikin mutanen har yanzu ana cigaba da kula da lafiyarsa a asibitin Gwamnati saboda Harbin da Akayi masa.
Umar ya bayyana cewa, Gwamnatin jahar Niger ta nuna jindadinta ga shuwagabanni hukomomin tsaro na jahar da kuma shuwagabanni yankunan ta yadda suka jajirce wurin kawo karshen matsalar rashin tsaro a wasu bangarorin jahar.
Tun da farko Jami’in hulda da jama’a na Rundunar yan sandan jahar, DSP Wasiu Abiodun, ya bayyana cewa jami’anmu hadin gwiwa da Yan kungiyar sa Kai, sun kubutar da mutane da aka kama sun kuma mayar dasu a yankunansu, bayan harin da aka Kai ranar Daren Juma’a.
A wani labarin, Ƴan Sanda a jahar plateau, sun Hana wani yunkurin kai Hari a kauyen Jebbu dake karamar hukumar Bassa.
Kwamishinan Ƴan sSandan Jahar, CP Bartolommeo N.Onyeka, ya bayyana cewa Yan sandan sun samu nasarar hana kai harin bayan samun Kiran wani daga cikin mazaunin yankin.
