Gabanin gasar wasannin cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2021 a Ƙasar Cameroon, Karuwai sun fitar sanarwar ƙara kuɗin farashin su, a yayinda suka bayyana cewa a shirye suke su cika muradun kwastomomin su a matakai daban-daban.
Karuwai a Ƙasar Cameroon sun fitar da sabon farashin gabanin gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2021, da zai fara a watan Janairun Shekarar 2022.
Gasar cin kofin wanda aka sanar cewa zai fara a tsakanin ƙarshen watan yuni zuwa Juli a manyan garuruwa guda biyar, dake da filin wasanni guda 6, zai wakana ne a watan Janairun Sabuwar Shekara a ranar 9, zai kuma ƙare a ranar 6 ga watan Fabrairu.
Duk da cewa, magoya baya da masu ruwa da tsaki da suka ziyarci gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar data gabata a Ƙasar Egypt, Basu damar shaƙatawa ba, tunda an hana karuwanci a Ƙasar, Ƙasar Cameroon ta bambanta da Egypt.
Dokar Ƙasar ta hana Karuwanci, amma ana gudanar da hakan a ƙarƙashin ƙasa, da gagarumar kasuwa.
Ga Farashin kamar haka
Saduwa guda ɗaya: daga Dala $30 an ƙara zuwa $40
Saduwa sau biyu: Dala $20 an ƙara zuwa Dala $70
Saduwa sau uku a dare ɗaya: daga Dala $40 zuwa Dala $100
Rabin dare daga Dala $70 zuwa Dala 130
Dare ɗaya: Dala $250
Wannan dai farashi wasu manyan Karuwai ‘Ashawo’ a Ƙasar Cameroon, Wanda ba’a ambata sunan su ba.

Gaskiya duniya tazo karshe su karuwai miye abun farashi su da ba sari su ke yi ba