Mu Muka Taimakawa Peter Obi Ya Zama Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa A LP – Sowore

Mu Muka Taimakawa Peter Obi Ya Zama Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa A LP – Sowore

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress, Omoyele Sowore, ya bayyana yadda ya taimaka wa dan takarar jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Sowore, yayin da yake magana a ranar Litinin din nan, a wajen taron tunawa da wani lauya kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Cif Gani Fawehinmi, wanda ya mutu, aka gudanar kuma a Legas, ya ce jam’iyyar LP, ta samu matsala wajen zaben Obi.

A cewarsa kamar yadda a can baya ake ta kiraye-kirayen cewa bai kamata a gabatar da Obi ba, amma a haka Sowore ya shige gaba wajen ganin ya samu wannan tikiti.

Sowore ya ce shi, tare da Babban Lauyan Najeriya kuma mai fafutuka, Femi Falana, sun tashi tsaye wajen daukar matakin kare LP, “Lokacin da jam’iyyar Labour ta shiga matsala.

Akwai wani dan jam’iyyar LP wanda ya dage cewa LP ba za ta iya gabatar da takarar Peter Obi ba., Bayan sun sami matsala ta shari’a.

Sowore ya ce Mun je domin ganin an yanke hukunci a kotu; daga Kotun Daukaka Kara, kuma ya mika ta ga Falana ya yi amfani da ita wajen kare jam’iyyar Labour, kuma ta hanyar tsawaita takarar Peter Obi.

Cif Fawehinmi, wanda har zuwa rasuwarsa marubucin Najeriya ne, mawallafi, mai sukar al’umma, kuma ɗan siyasa ana jin daɗin tunawa da shi saboda fafutuka da kare talaka a gaban kotu.

Fwehinmi ya zama SAN a cikin Satumba 2001 kuma an ba shi Babban Lauyan Mass a Jami’ar Obafemi Awolowo a 1988, tare da sauran kyaututtuka na duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *