Mayaƙan Boko Haram 17 Sun Miƙa Wuya Ga Rundunar Soji

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ‘yan ta’addar Boko Haram goma sha bakwai da suka hada da iyalansu sun mika wuya ga sojojin Bataliya ta 151.

Jami’an sune wadanda aka tura zuwa lBanki-Junction a karamar hukumar Bama a jihar Borno.

Rundunar ta bayyana hakan ne a ranar Talata ta shafinta na Twitter tana mai cewa, yawan mika wuya da ‘yan ta’addan da iyalansu suke yi, ya biyo bayan wani sabon farmakin da dakarun soji na Operation Hadin Kai suka kai a yankin Arewa maso Gabas.

A cewar rahotanni, wani babban mai zartar da hukuncin kisa na bangaren Shekau, Bashir Bulabuduwaye, ya mika wuya ga sojojin Najeriya kwanan nan.

Bulabuduwaye, tare da matansa da ‘ya’yansa, an ce sun mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai da ke Baking a karamar hukumar Bama a jihar Borno.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *