A ci gaba da kokarin sasanta rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, a yau Talata ne kwamitin amintattu na jam’iyyar zai gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a Fatakwal.
Za a gudanar da taron ne a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal da karfe 12 na rana.
Wani babban jami’in jam’iyyar a jihar da bai so a ambaci sunansa ba ya tabbatar wa da wakilinmu a safiyar ranar Talata.
Ana sa ran mutanen Wike da gwamnonin Enugu, Abia, Benue, Oyo, da kuma wasu manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar za su halarci taron.
Gwamna Wike da wasu gwamnonin yankin Kudu sun kauracewa yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.
Don haka, ana sa ran za a tattauna a taron da nufin samun matsaya guda don kwantar da hankalin Wike da mutanensa yayin da zaben 2023 ke kara kusantowa.
Gwamna Wike da wasu takwarorinsa hudu, wadanda a yanzu ake kira da manyan gwamnoni biyar, sun kulla kawance domin neman daidaito da adalci a jam’iyyar.
