Ƴan Bindiga Sun Sako Ragowar Fasinjojin Jirgin Ƙasan Abuja-Kaduna
’Yan bindiga sun sako fasinjoji 23 da suka rage a hannunsu daga cikin mutanen da suka yi garkuwa da su a Jirgin Kasan Abuja-Kaduna.
Hedikwatar Tsaro ta Najeriya ta tabbatar cewa a ranar Laraba da La’asar ne aka mika fasinjojin su 23 ga Kwamitin Shugaban Kasa da Babban Hafsan Tsaro, Janar Lucky Irabor, ya kafa.
A ranar 28 ga watan Maris, 2022 ne ’yan ta’addan Boko Haram suka kai harin bom kan jirgin kasan da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja inda suka kashe akalla mutum tara, suka yi awon gaba da wasu kimanin 60
