Wata Gobara Ta Ƙone Zauren Majalisar Dokokin Jihar Kogi

Wuta ta kone dakin taro na majalisar dokokin jihar Kogi da sanyin safiyar ranar Litinin din nan.

Ba a gano musabbabin tashin gobarar ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.

Daraktan hukumar kashe gobara ta Kogi, Salau Ozigi, ya ce gobarar ba ta wuce dakin taro da dakin hoton.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Prince Mathew Kolawole, kakakin majalisar, ya dora alhakin faruwar lamarin da yin zagon kasa, ya kuma ce jami’an tsaro za su binciki lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *