Hisba Ta Damƙe Karuwai 25 Da Masu Sayar Da Giya A Jigawa
Rundunar Hisba ta jihar Jigawa ta kama mata masu zaman kansu guda 25 a karamar hukumar Kazaure.
Kakakin hukumar ta Hisba, Muhammad Sale Korau ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa DAILY POST.
Ya bayyana cewa, kwamandan Hisba na jihar ya jagoranci samamen tare da samun nasarar cafke mutane talatin da daya a karamar hukumar Kazaure.
Ya ce wadanda aka kama sun hada da, Karuwai 25, da wasu maza shida bisa zargin sayar da barasa a Gada a Kazaure.
Rundunar, duk da haka, ta nanata kudurinta na yakar duk wata munanan dabi’u a jihar.
Ya ce an mika wadanda ake zargin ga ‘yan sanda domin gudanar da bincike
