Shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu ya musanta zargin da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike ya yi na karbar naira biliyan daya daga hannun wani gwamnan jam’iyyar.
Wike ya yi wannan zargin ne yayin wani taron manema labarai a ranar Juma’ar nan a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Amma Ayu ya ce bai taba karbar kudi a matsayinsa na mutum ba, ya kara da cewa kudaden da aka karba a madadin jam’iyyar an mayar da su bisa ka’ida a ma’ajiyar jam’iyyar ta PDP.
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Sai dai ya bayyana cewa wani gwamnan jam’iyyar ya bayar da gudummawar Naira Miliyan 100 don gyaran c ibiyar Dimokuradiyya ta PDP, kuma kudin ba su ma kare ba saboda ana ci gaba da gyaran.
