Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin fara jigilar mahajjatan kiristoci daga Najeriya kai tsaye zuwa Isra’ila.

Za a sadaukar da jiragen ne don jigilar mahajjatan Kirista zuwa birnin Kudus bisa hadin gwiwa da kamfanin Air Peace, babban kamfanin jirgin saman Najeriya.

Daily Trust a ranar Lahadin da ta gabata ta ruwaito cewa, wannan shi ne karon farko cikin lokaci mai tsawo da za a yi jigilar alhazan Kirista kai tsaye zuwa Isra’ila.

Sakataren zartarwa na Hukumar Kiristoci na Najeriya, Christian Pilgrim Commission, Rev Dr Yakubu Pam, ya yi nuni da cewa a karshen watan Nuwamba, 2022, za a fara jigilar jirage kai tsaye daga Najeriya zuwa Isra’ila.

Najeriya, H.E Mr Michael Freeman da shugaban Air Peace, Mista Allen Onyema a ofishinsa da ke Abuja.

Sanarwar da Air Peace ta fitar ta nakalto shugaban kamfanin na bada tabbacin a shirye ta ke ta fara gudanar da ayyukan jirgin kamar yadda hukumar ta ce za ta inganta zirga-zirgar jiragen kai tsaye zuwa Isra’ila.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *