APC Ta Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Soke Ɗan Takarar Ta A Jihar Adamawa

APC Ta Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Soke Ɗan Takarar Ta A Jihar Adamawa

 

Jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke na hana jam’iyyar tsayar da ‘yar takarar gwamna a zaben 2023 mai zuwa.

A ranar Juma’a ne kotun ta soke takarar Sen. Aishatu Ahmed, tare da hana ta bayyana kanta a matsayin ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar APC, bisa karar da Malam Nuhu Ribadu, tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon-kasa ya shigar, yana kalubalantarta.

Sakamakon zaben fidda gwani na takarar gwamnan jihar Adamawa na jam’iyyar APC a ranar 26 ga watan Mayu, bisa zargin iyaka kan zabe, sayen kuri’u da sauran kura-kurai.

Mai shari’a Abdulaziz Anka, a hukuncin da kotun ta yanke bayan ya warware duk wasu batutuwan da za a duba a cikin wata kwakkwarar karar, ya ce zaben fidda gwani na gwamnan APC na Adamawa bai bi dokar zabe ta 2022, kundin tsarin mulkin kasa, da ka’idojin jam’iyyar ba.

Don haka, kotun ta ce nadin Sanata Aishatu Ahmed da wanda ake kara na daya, APC ta yi, ba shi da inganci, kuma ba bisa ka’ida ba, domin a fili ya ci karo da sashe na 85 (5) na dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima, don haka ba za a iya gabatar da da ita ba a matsayin yar takarar da zata shiga zaben 2023 mai zuwa.

Sai dai jam’iyyar APC reshen jihar Adamawa da ta taso daga taron kwamitin ayyuka na jihar da dukkan shugabannin kananan hukumomi sun sha alwashin daukaka kara kan hukuncin bayan sun yi fatali da hukuncin.

Dr Raymond Chidama, sakataren jihar wanda ya karanta sanarwar da ke kunshe da matsayin jam’iyyar bayan kammala taron, ya bukaci ‘yan jam’iyyar su kwantar da hankalinsu.

Ya ce jam’iyyar za ta shiga zaben fidda gwani na gwamna da ke tafe tare da bayyana kyakkyawan sakamako na karar da jam’iyyar za ta shigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *